News
‘Yan Sanda Sun Cafke Mutum Biyu Da Wayoyin Sata Na Miliyan 35 A Maiduguri
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Borno ta samu gagarumar nasara a kokarinta na yaki da aikata laifuka, inda ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da satar wayoyin hannu na miliyoyin naira a Maiduguri.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana cewa an kama Ba’isa Yerima (25) da Lawan Yusuf (26) dauke da wayoyin hannu guda 61 da kudinsu ya kai Naira miliyan 35.
A cewarsa, an cafke su ne a ranar 15 ga Maris, bayan samun bayanan sirri da suka jagoranci jami’an sashin kula da satar wayoyi zuwa yankin Polo, inda aka kama su da wayoyi da ake zargin sun sata.
Ya kara da cewa daga cikin wayoyin da aka gano, guda bakwai sun kasance cikin rahoton sata, kuma ana ci gaba da kokarin mayar da su ga masu su.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Yusufu Mohammed Lawal, ya jaddada aniyar rundunar na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da yin kira ga duk wanda aka sace masa waya da ya tuntubi rundunar don samun hakkinsa.
-
News6 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News5 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News4 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
