News
Kisan Gilla: Gwamnatin Kano Ta Ya Bawa Shugaba Tinubu Da Gwamnan Edo Kan Daukar Mataki
Gwamnatin Jihar Kano ta gode wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Gwamnan Jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, bisa gaggawar ɗaukar matakin da suka yi bayan kisan gillar da aka yi wa mutane 16 ’yan asalin Kano a Udene, Ƙaramar Hukumar Uromi ta Jihar Edo.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bukaci a gudanar da shari’a ta gaskiya tare da bayyana wadanda aka kama a fili, domin tabbatar da adalci.
“Azumin Sitta Shawwal: Fa’idodi, Sharudda, Da Muhimmancinsa A Musulunci”
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai, Kwamared Ibrahim Waiya, ya fitar, Gwamnan ya yaba da irin azamar Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Edo wajen tuntuɓar Gwamnatin Kano tare da jajantawa iyalan waɗanda suka rasa ransu.
Hakazalika, ya gode wa Gwamnan Edo bisa tattaunawa da al’ummar Hausawa da ke jihar tare da alƙawarin biyan diyya ga iyalan mamatan.
Bugu da ƙari, Gwamnan ya jinjina wa Shugaba Tinubu bisa umarnin da ya bai wa hukumomin tsaro na binciken waɗanda suka aikata wannan ta’asa, yana mai cewa hakan na nuna kwazon Gwamnatin Tarayya wajen kare rayukan ‘yan Najeriya.
Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da sanya ido don ganin an yi adalci da kuma tabbatar da an biya diyya ga iyalan waɗanda suka rasa ransu.
