Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Rufe Kamfanoni 9 Saboda Kin Biyan Haraji

Published

on

Hukumar Kula da Haraji ta Jihar Kano (KIRS) ta kulle manyan kamfanoni tara da suka haɗa da cibiyoyin kasuwanci, makarantu masu zaman kansu da kuma wasu cibiyoyin hada-hadar kuɗi, saboda ƙin biyan harajin da ya wajaba a kansu.

Wannan mataki ya biyo bayan gazawar kamfanonin wajen biyan bashin haraji duk da samun sakonnin tunatarwa da dama daga hukumar. KIRS ta ce ta bi dukkan hanyoyin doka kafin ɗaukar wannan mataki, ciki har da samun sahihin umarnin kotu.

Advertisement

Yadda Najeriya Da Gwamnatin Sojin Ƙasar Nijar Sun Sasanta.

Shugaban tawagar da ta jagoranci aikin rufe kamfanonin, Abbas Sa’idu, ya ce hukumar ta KIRS ta gaji da ƙin amsa gayyatar da aka tura wa kamfanonin don sasanta batun harajin da suke bi.

“Mun bi dukkan hanyoyin lumana kafin zuwa wannan mataki. Amma da ya bayyana cewa kamfanonin ba sa da niyyar biyan harajin, sai muka nemi umarnin kotu domin tabbatar da doka da oda,” in ji shi.

Advertisement

Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar na ƙoƙarin dakile asarar kuɗaɗen shiga domin ƙarfafa tattalin arzikin jihar.

Daraktan ya bayyana cewa gwamnatin Kano karkashin shugabancin gwamna Abba Kabir Yusuf ta jajirce wajen ganin an cika dukkan haƙƙoƙin gwamnati na haraji. Ya ce biyan haraji na taimakawa wajen gina ababen more rayuwa da inganta ayyukan ci gaba.

Advertisement

“Muna da cikakken shiri wajen tabbatar da bin doka. Ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wanda ke kaucewa biyan haraji,” in ji shi.

Hukumar KIRS ta jaddada cewa za ta ci gaba da ɗaukar matakai na doka ga duk wani kamfani ko mai kasuwanci da ke kaucewa biyan haraji, tare da jan hankalin masu ruwa da tsaki da su bi doka da oda.

Advertisement

Ta kuma bukaci ‘yan kasuwa da sauran kamfanoni su tabbatar da cewa sun biya dukkan harajin da ya rataya a wuyansu kafin hukumar ta ɗauki mataki makamancin haka.

Masana tattalin arziki sun bayyana matakin a matsayin muhimmin ci gaba da zai taimaka wajen sanya ido kan yadda ake tafiyar da harkokin kuɗi a jihar, tare da tabbatar da gaskiya da adalci a cikin tsarin gwamnati.

Advertisement

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar ke ƙarfafa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga daga cikin gida, domin rage dogaro da kuɗaɗen gwamnatin tarayya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending