Connect with us

News

Turji Ya Tilasta Wa Mutane Fiye Da 5,000 Yin Hijira A Sokoto

Published

on

AA 31108279

Fiye da mutane 5,000 daga ƙauyuka sama da 12 sun tsere daga gidajensu a Jihar Sokoto, sakamakon barazanar da wani gawurtaccen ɗan bindiga, Bello Turji, ya yi musu.

Wannan na zuwa ne bayan Turji ya umarci mazauna ƙauyukan da ke gundumar Isa su bar muhallansu ko kuma su fuskanci kisa.

Advertisement

Wani ɗan majalisar jihar, Habibu Halilu Modachi, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, “Tsakanin Asabar da Lahadi, fiye da mutum 5,000 ne suka tsere daga kauyukansu a Bafarawa da wasu ƙauyuka a kusa, bayan Turji ya aika da saƙon barazana cewa su fice kafin Lahadi da rana ko kuma a kashe su.”

Shan Kwaya Ta Komawa Lemun Kwalba: Sabuwar Dabia da Ke Barazana ga Rayuwar Matasa

Ya ce aƙalla mutum 12 ne aka kashe a hare-haren da aka kai, kuma akwai yiwuwar adadin ya karu, kasancewar rahotanni na ci gaba da fitowa daga yankin.

Advertisement

Rahotanni sun ce mazauna ƙauyukan sun tsere zuwa garuruwan Isa da Shinkafi da ke Jihar Zamfara da wasu wuraren da suka fi kwanciyar hankali.

Wani da ya tsere daga ɗaya daga cikin ƙauyukan, Ahmad Abdullahi, ya ce ‘yan bindigar sun shigo suna harbin sama tare da karɓe duk wata dukiya da suka tarar.

Advertisement

“Suna kwashe kudi, kayan abinci, da duk wani abu mai daraja,” in ji shi.

Modachi ya ƙara da cewa, “Ko da safiyar Litinin, ‘yan bindigar sun sake kashe mutane biyu, sun ji wa tara rauni, sannan sun yi garkuwa da bakwai.”

Advertisement

An dai dade ana zargin Bello Turji da kai hare-hare a jihohin Zamfara da Sokoto. Ya koma ayyukan ta’addanci tun bayan da ya bar kiwo a 2011, inda ya tsunduma fashi da makami da garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa.

Turji ya taba shiga yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin Zamfara, amma daga baya ya karya alkawarin tare da ci gaba da kai hare-hare a sassa daban-daban na yankin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending