Connect with us

News

Shan Kwaya Ta Komawa Lemun Kwalba: Sabuwar Dabia da Ke Barazana ga Rayuwar Matasa

Published

on

images (2)

Wani sabon salo na ta’ammali da kayan maye ya ɗauki hankalin jama’a — shan sinadaran maye da aka gauraya da lemun kwalba. Wannan dabi’a na kara yaduwa a tsakanin matasa, musamman ‘yan makaranta da masu yawo-yawo a gari.

A kallo na farko, lemun kwalban tamkar abin sha ne mai sanyi da nishaɗi. Amma fa, kurɓa ɗaya na iya jefa rai cikin haɗari — gusar da hankali, mantuwa, ko ma haɗa gado da asibiti.

Advertisement

Matashi Ya Kashe Saurayin ’Yar Uwarsa A Kano

Wasu daga cikin matasan da ke sha, ba su ma san me ke cikin abin ba. Suna ganin kamar nishaɗi ne kawai, amma suna barin rayuwarsu cikin hatsari.

Haka zalika FRI HAUSA ta ruwaito cewa wannan dabia tana iya haifar da ciwon kwakwalwa, bugun zuciya, ko mutuwa.

Advertisement

Lamarin ya kai har ana sha a cikin ajujuwa, a layukan ‘yan haya, da ma a zauren gidaje. A wasu lokuta, ana raba irin waɗannan abubuwa a bukukuwa da tarurruka, ba tare da sanin iyaye ko malamai ba.

Al’umma na kara nuna damuwa, yayin da wasu ke ganin idan ba a ɗauki mataki ba yanzu, nan gaba matsalar za ta fi ƙarfin hukuma. Shugabannin addini, na al’umma da masu ilimi na kira da a tashi tsaye don fatattakar wannan muguwar dabia.

Advertisement

Wannan matsala ta zama barazana ga kimar jama’a, abin da ya sanya ma masu ruwa da tsaki ke ci gaba da jan hankalin cewa, lokaci ya yi da iyaye, malamai, shugabanni da al’umma za su tashi tsaye, domin kawo ƙarshen wannan ƙalubale.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending