Connect with us

News

An Gurfanar Da Magidanci A Kotu Kan Daba Wa Surukinsa Kwalba

Published

on

Kwalba

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

An gurfanar da wani magidanci a gaban wata Kotun Majistare mai zamanta a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun, kan zargin daba wa surukinsa kwalba a kai.

 

Advertisement

Lauyan mai gabatar da kara, Sufeta Evelyn Motim, ta fada wa kotun cewa, mai kare kansa ya aikata laifin ne ranar 30 ga watan Oktoba a yankin Abule Ijaye da ke jihar.

Kasar Dubai Ta Dakatar Da Zirga-zirgar Jirage Zuwa Najeriya sai illa Masha Allah

Advertisement

 

Ta ce wanda ake zargin ya daba wa mahaifin matarsa wata fasasshiyar kwalba a kai.

Advertisement

 

Ta ce surukin ya gamu da iftila’in ne bayan da aka gayyato shi don ya zo ya sasanta matsalar aure, daga nan wanda ake zargi ya hada baki da wasu suka lakada wa surukin duka.

Advertisement

 

Lauyar ta ce wannan laifi ne da ya saba wa sassa na 516 da 355 na Kundin Dokokin Manyan Laifuka na Jihar Ogun na 2006.

Advertisement

 

Alkalin kotun ya ba da umarnin a kai wanda ake zargin kurkuku a ajiye zuwa lokacin da zai biya kudin beli N50,000 da aka yanka masa da kuma shaida daya.

Advertisement

 

Daga nan, ya dage shari’ar zuwa 23 ga Nuwamba don yanke hukunci.

Advertisement

 

(NAN)

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending