Connect with us

News

Farfesa Gwarzo Ya Bai Wa Kwalejin Sa’adatu Rimi Motar Dalibai Mai Kujeru 60

Published

on

Spread the love

Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, wanda shi ne wanda ya kafa kuma shugaban kungiyar jami’o’in MAAUN, ya kyautar wa Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kumbotso, Kano, babbar mota mai daukar dalibai 60.

Farfesa Gwarzo ya bayyana hakan ne a lokacin da ya jagoranci wasu daga cikin jami’an gudanarwar MAAUN zuwa ziyarar girmamawa ga sabon Provost na kwalejin, Dokta Kabir Ahmad Gwarzo, a ranar Alhamis.

Yadda Tinubu Da Barau Suka Taimaka Wajen Kafa Rundunar Tsaron Daji A Najeriya

A yayin ziyarar, Farfesa Gwarzo ya taya sabon shugaban kwalejin murna bisa nadin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi masa, yana mai cewa wannan tallafi wani bangare ne na jajircewarsa wajen bunkasa harkar ilimi a Kano da ma Najeriya baki daya.

Ya ce jami’ar MAAUN na da kudurin ci gaba da hada gwiwa da kwalejin domin taimaka mata wajen cimma manufofinta na bayar da ingantaccen ilimi.

Advertisement

Farfesan ya yaba da kwarewar sabon Provost din, yana mai bayyana shi a matsayin masani nagari da gogaggen ma’aikacin ilimi da zai iya ja wa kwalejin ci gaba.

Ya kara da cewa nadin da aka yi wa Dokta Kabir na bisa cancanta ne, inda ya yi amannar cewa za a ga canji a harkokin gudanarwar kwalejin.

A nasa bangaren, Dokta Kabir Ahmad Gwarzo ya bayyana godiyarsa bisa wannan taimako, yana mai cewa MAAUN ta dade tana tallafa wa manyan makarantu a fadin kasar nan.

Ya jinjina wa Farfesa Gwarzo bisa kokarinsa wajen gyara tsarin ilimi da kuma ba matasa da mata dama domin taka rawar gani a cigaban al’umma.

Advertisement

A baya, gidauniyar Adamu Abubakar Gwarzo Foundation ta raba irin wannan kyauta ga wasu cibiyoyi, ciki har da Kaduna Polytechnic, Al-Istiqama University ta Sumaila, Federal University Dutsin-Ma, Bayero University Kano, da North West University Kano.

Sauran da suka ci gajiyar tallafin sun hada da Dan Dicko Dankoulodo University da ke Maradi a Nijar, Aliko Dangote University of Science and Technology ta Wudil, da Federal Polytechnic Kabo.

 

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *