News
Hawan Jini: Gwamnatin Kano Ta Kara Kaimi Wajen Yaki Da Cututtuka Masu Zaman Kansu
Gwamnatin Jihar Kano ta ce tana ci gaba da ɗaukar matakai na musamman don yaki da cututtuka masu zaman kansu, musamman ciwon hawan jini, wanda ke daga cikin cututtukan da ke yawan hallaka mutane cikin shiru.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar a Asibitin Koyarwa na Muhammadu Abdullahi Wase da ke Kano, a ranar Juma’a.
Farfesa Gwarzo Ya Bai Wa Kwalejin Sa’adatu Rimi Motar Dalibai Mai Kujeru 60
Ya ce ciwon hawan jini na daga cikin manyan cututtuka da ke kashe mutane ba tare da alamomi masu yawa ba, inda ya bayyana shi a matsayin “makashin shiru”.
Taken Ranar Ciwon Hawan Jini ta Duniya ta bana shi ne: “Auna Jinin Ka daidai, Sarrafa Shi, Rayu Tsawon Lokaci!”, wanda ke jaddada bukatar duba jini akai-akai, kiyaye lafiya da bin tsarin rayuwa mai tsafta.
Horaswa da Fadada Cibiyoyi
Kwamishinan ya ce tun bayan hawar Gwamna Abba Kabir Yusuf kan mulki, gwamnatin ta horar da ma’aikatan lafiya 412 a cibiyoyin lafiya 208 a fadin jihar, tare da fadada cibiyoyin da ke kula da ciwon hawan jini daga 52 zuwa 260.
Baya ga haka, an haɗa kula da ciwon hawan jini da cututtukan kwakwalwa domin marasa lafiya su samu cikakken kulawa a lokaci guda.
Tantance Lafiya
A karkashin shirin “Project 10 Million”, an tantance lafiyar dubban jama’a a cikin mako guda, inda aka gano mutane 26,000 na fama da ciwon hawan jini, yayin da wasu 5,000 ke dauke da ciwon sikari. An fara ba su magani kyauta.
Haka kuma, gwamnatin ta kaddamar da shirye-shiryen “Abba Care Support Program” don masu fama da sikila da kuma “Abba Gida-Gida Diabetic Support Program” don yara da ke fama da ciwon sikari nau’i na farko. Shirye-shiryen na bayar da magunguna da na’urorin gwaji kyauta.
Kiran Gwamnati Ga Jama’a
Dr. Yusuf ya bukaci al’umma da su dinga duba jinin su akai-akai, su kauce wa cin abinci mai yawan gishiri da mai, tare da bin hanyoyin kiyaye lafiya.
Ya kuma yaba wa ma’aikatan lafiya da kafafen watsa labarai, da abokan hulda kamar WHO, UNICEF, PROJECT HOPE da Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya bisa goyon baya
n da suke ba wa jihar Kano.
