Sports
Hatsarin Mota Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 21 Daga Tawagar Wasannin Kano

Akalla mutane 21 daga cikin tawagar da ta wakilci jihar Kano a gasar wasanni ta ƙasa da aka gudanar a jihar Ogun sun rasa rayukansu, bayan da motar da suke ciki ta yi mummunan hatsari a hanyarsu ta dawowa gida.
Rahotanni sun nuna cewa kimanin motocin bas guda 30 ne suka ɗauki ‘yan wasan jihar Kano daga Ogun, inda suka bar jihar da yammacin Alhamis, kuma suka iso Kano lafiya—banda motar ƙarshe da ta gamu da haɗari.
Maƙabartar Kuka Bulukiya Ta Zama Mafakar ’Yan Daba a Cikin Birnin Kano
Wani daga cikin jami’an tafiyar, Ado Salisu, ya shaida wa DAILY NIGERIAN cewa hatsarin ya faru ne da misalin karfe 8:00 na safiyar Asabar, a kan gadar Daka Tsalle da ke cikin ƙaramar hukumar Garun Malam.
“Motar ta faɗa wani rami ne sannan ta wuntsila, wanda hakan ya janyo mutuwar mutane 19 nan take, yayin da wasu biyu kuma suka rasu a babban asibitin Kura,” in ji Salisu.
Ya ƙara da cewa, daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu har da kakakin hukumar wasanni ta jihar Kano, Ibrahim Galadima.
A halin yanzu, sama da mutum goma sun samu raunuka kuma suna karɓar kulawa a asibiti, yayin da hukumomi ke ci gaba da shirye-shiryen miƙa gawarwakin ga iyalan mamatan.
Hatsarin ya haifar da alhini da jimami a fadin jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya, musamman a tsakanin masoya wasanni da iyalan waɗanda lamarin ya shafa.