Connect with us

News

‎Ta Yaya Zuciyarka Za Ta Samu Kwanciyar Hankali Da Wahala?

Published

on

IMG 20250429 WA0017~2

‎Idan kana da yakinin cewa Allah ne Maɗaukakin Sarki ne Ya halicce ka, kuma kana kokarin rayuwa bisa tafarkinSa – tafarkin gaskiya, adalci da tausayi – to ya kamata zuciyarka ta ji raɗaɗin halin da duniya ke ciki.

‎Yau a kowace ƙasa da ke cikin duniya, musamman namu Najeriya, rayuwa ta koma tamkar gwagwarmayar tsira. Yara na kwana da yunwa, matasa sun rasa makoma, dattawa na neman magani babu mafita. Me ya jawo haka? Rashin shugabanci na gari. Rashin shugabannin da ke da tausayi, da adalci, da gaskiya.

Yadda Jirgin Soji Ya Kashe ’Yan Sa-kai 20 A Zamfara Bisa Kuskure

‎Yana da matuƙar ban mamaki yadda wasu mutane ke jin daɗin rayuwa alhali mafi yawan jama’a na cikin azaba. Yaya aka yi muka kai ga wannan matsayin da ake kallo zalunci, cin hanci, da son zuciya a matsayin ruwan dare?

‎Wani matashi mai hangen nesa ya ce:

‎“Na gane cewa idan ban tashi tsaye na yi wani abu domin kawo sauyi ba, to zan rayu cikin nadama, in mutu cikin kunya – kunya a wurina, da kuma a gaban al’umma da tarihin duniya.”

‎Wannan faɗa ba ƙarya ba ne. Rayuwa ba ta canzawa sai mutum ya canza ta da kansa. Ba lallai sai ka zama shugaban ƙasa ko ɗan majalisa ba kafin ka zama mai tasiri. Abu mafi muhimmanci shi ne fahimtar cewa kana da rawar da za ka taka wajen ganin al’umma ta samu walwala.

Advertisement

‎Sauyin da muke so yana farawa ne da tunanin mutum. Idan kowa zai ce “zan ɗauki nauyin gyaran da ke gabana,” to da sannu abubuwa za su gyaru. Amma idan muka ci gaba da kallon abubuwa suna lalacewa, muna cewa ba namu ba ne, to za mu ci gaba da rayuwa cikin ƙunci, mu mutu cikin kaskanci.

‎A ƙarshe: Idan kana gaskiya da Allah, to zuciyarka ba za ta huta ba yayin da jama’a ke wahala. Ba za ka zauna lafiya ba alhali shugabanninmu ba sa yin adalci. Dole ne mu farka, mu fahimta, mu tashi tsaye. Domin duniya ba za ta gyaru da addu’a kawai ba – sai an haɗa da aiki.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending