Connect with us

News

Tsohon Ministan Ilimi Farfesa Jibril Aminu, Ya Rasu  Yana Da Shekaru 85 A Duniya.

Published

on

Tsohon Ministan Ilimi da Sanata, Farfesa Jibril Aminu, Ya Rasu

Babban masani a fannin likitanci kuma tsohon Ministan Ilimi da Fetur, Farfesa Jibril Muhammad Aminu, ya rasu yana da shekaru 85 a duniya.

Farfesa Aminu ya rasu ne a ranar Alhamis a birnin Abuja, bayan fama da jinya da ya ɗauki lokaci yana yi. Marigayin ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ’yan siyasa da masana a fannin ilimi da kiwon lafiya a Najeriya.

Advertisement

‎Matasa A Guji Duk Wani Abu Da Ka Iya Tayar Da Hankali A lokacin bukukuwan Sallah ‎ ‎ ‎—Cewar Sarkin Jinkan Hausawan Afrika

A lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya riƙe muƙamin Jakadan Najeriya a ƙasar Amurka tsakanin shekarar 1999 zuwa 2003. Daga nan kuma aka zaɓe shi a matsayin Sanata mai wakiltar mazabar Adamawa ta Tsakiya daga 2003 zuwa 2011.

Farfesa Aminu ya bar tarihin nagarta da kishin ƙasa, inda ya taka muhimmiyar rawa a harkokin ilimi, diflomasiyya da kuma majalisar dokoki.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending