News
Matasa A Guji Duk Wani Abu Da Ka Iya Tayar Da Hankali A lokacin bukukuwan Sallah —Cewar Sarkin Jinkan Hausawan Afrika
Sarkin Jinkan Hausawan Afrika, Ambasada Ibrahim Ali Ibrahim (Abba Alra-iwas), ya bukaci matasa da daukacin al’ummar Hausawa da su kasance masu nuna da’a da kwarewar zaman lafiya a lokacin bukukuwan Sallah da ke karatowa.
Sarkin ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da ya yi da wakilan Jaridar INDA RANKA, inda ya bayyana damuwarsa kan yadda ake samun wasu rikice-rikice da tashin hankali a lokutan shagulgulan sallah.
Jigawa: Gwamnati Ta Bankado Ma’aikatan Bogi 7,000 Da Ke Karɓar Albashi
“Lokacin Sallah lokaci ne na ibada da godiya ga Ubangiji, ba lokacin tada hankali ko tayar da kura ba. Muna rokon matasa da su dauki wannan lokaci a matsayin damar nuna kwarewar tarbiyya da da’a, ba barna da tada hankali ba,” in ji Sarkin.
Ya ce, matsalolin da ake fuskanta a wasu lokuta na da nasaba da rashin tarbiyya da shaye-shaye, wanda hakan ke janyo rigingimu da rashin kwanciyar hankali a wuraren taron jama’a. Ya bukaci iyaye da shugabannin al’umma da su kara sa ido a kan tarbiyyar matasa domin gina al’umma mai tsafta da hadin kai.
Sarkin Jinkan ya kuma yaba wa hukumomin tsaro kan yadda suke kokari wajen tabbatar da tsaro a lokutan sallah, yana mai cewa, “Ya kamata a kara sanya ido da wayar da kan jama’a domin ganin an gudanar da bukukuwan sallah cikin kwanciyar hankali da lumana.”
Ya kuma roki Allah ya kawo zaman lafiya da dauwamammen hadin kai a tsakanin al’ummar Hausawa da ma sauran kabilun Afrika, yana mai jan kunnen matasa da cewa, “Zamani ya sauya, dole ne mu sauya tare da shi domin amfanar da kanmu da zuriyarmu.”
