Sports
Usman Abdallah Ya Ajiye Aikin Horar Da Kano Pillars

Babban kocin ƙungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Usman Abdallah, ya ajiye aikinsa na horas da tawagar a ranar Laraba, kamar yadda sashen yaɗa labarai na ƙungiyar ya tabbatar da hakan.
Sanarwar da aka fitar da yammacin ranar Laraba ta bayyana cewa Abdallah ya yanke shawarar barin mukaminsa ne da kansa, sai dai bai bayyana dalilan da suka sanya shi ɗaukar wannan mataki ba.
A halin da ake ciki, magoya bayan Pillars na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu a kafafen sada zumunta dangane da ficewar Abdallah, inda da dama ke bayyana fatan ganin sabon babi mai armashi a tarihin ƙungiyar.