News
Jihar Kano Ta Musanta Zargin Karɓar Sabon Bashin Dala Miliyan 6.6 Daga Ƙasashen Ƙetare
Gwamnatin Jihar Kano ta karyata zargin da wata ƙungiya ke yadawa cewa ta karɓi sabon bashi na dala miliyan 6.6 daga ƙasashen ƙetare, tana mai bayyana labarin a matsayin ƙaryar ƙage da ke da nufin jefa al’umma cikin rudani da haifar da cece-kuce a fagen siyasa.
Cikin wata sanarwa da Darakta Janar na Hukumar Kula da Basussuka ta Jihar Kano, Malam Hamisu Sadi Ali, ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa babu wani bashi irin haka da aka taɓa karɓa tun lokacin da gwamnatin yanzu ta hau mulki a shekarar 2023.
Gwamnatin Kano Ta Ce Ba Ta Karɓi Sabon Bashi Na Dala Miliyan 6.6 Ba
Ya ce bisa tanadin doka, duk wani lamuni da gwamnatin jiha ke buƙata, dole sai ya bi matakan doka ta hannun hukumar da ke kula da lamuni, musamman idan bashi ne daga ƙasashen waje.
Sanarwar ta bayyana cewa rahoton da jaridar Daily Nigerian ta wallafa a ranar 11 ga Yuni, wanda ya fito daga wata ƙungiya mai suna APC Patriotic Volunteers, ya zargi gwamnatin NNPP da karɓar bashi daga ƙetare, wanda sanarwar ta bayyana a matsayin “rahoton da aka ƙulla domin biyan bukatun siyasa.”
Gwamnatin ta nuna mamaki bisa yadda shugaban ƙungiyar, Alhaji Usman Alhaji – wanda shi ne tsohon Sakataren Gwamnatin Jiha – ke yarda da irin wannan zargi, alhali yana daga cikin wadanda suka kafa dokar da ta samar da hukumar da ke kula da duk wani bashi a jihar.
> “Ko dai bai fahimci dokar da suka kafa ba, ko kuma siyasa ce kawai ke rinjayar shi,” in ji sanarwar.
Gwamnatin ta nanata cewa tun bayan da ta hau karagar mulki, ba ta karɓi wani sabon bashi ba, sai dai tana kokarin biyan dimbin basussukan da gwamnatin baya ta bar wa jihar karkashin tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
“A matsayinta na hukuma mai alhakin kula da lamuni a Jihar Kano, babu wani lamuni da aka karɓa ba tare da saninmu da amincewarmu ba,” in ji Ali.
Ya shawarci al’umma da su yi watsi da rahoton da ya kira da ƙarya tsagwaron gaskiya, yana mai cewa aikin jarida na gaskiya ya kamata ya kasance abin dogaro ne, ba na yaɗa ƙaryar da za ta haifar da rudani ba.
