News
IPMAN Za Ta Hana Tankokin Mai Ɗaukar Sama Da Lita 45,000 Daga Watan Oktoba
Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Ƙasa (IPMAN) ta sanar da cewa daga ranar 1 ga watan Oktoba, 2025, an haramta ɗora fiye da lita 45,000 na mai a kowanne tankar mai a Najeriya. Wannan mataki na daga cikin shirin da ake yi domin rage yawaitar haɗurra da kuma lalacewar tituna da ake fuskanta sakamakon lodin da ya wuce kima.
Shugaban IPMAN na Yammacin Najeriya, Chief Oyewole Akanni, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar daga Ibadan, inda ya ce matakin ya samo asali ne bayan wata ganawa ta musamman da aka yi tsakanin kungiyoyin masu ruwa da tsaki, da suka haɗa da PTD, NARTO, NMDPRA, da wakilan dillalan mai.
Kwamishinan Kano Ya Karɓi Dala $30,000 Kafin Tsayawa Dillalin Kwayoyi A Kotu —Rahoton DSS
> “Wasu daga cikin wadannan tankoki suna ɗaukar lita 90,000, wanda ya fi ƙarfinsu. Wannan lodin ya saba da ƙirar motar da kuma dokokin zirga-zirga, sannan yana haifar da manyan matsaloli kamar lalata hanyoyi da haddasa haɗurran mota,” inji Chief Akanni.
A cewar Akanni, daga cikin sabbin matakan da za a fara aiwatarwa akwai wajabcin saka murfin tsaro a kan kowanne tankar mai domin hana zubar da man a yayin hatsari. Haka zalika, an hana direbobin tankokin man zirga-zirga tsakanin ƙarfe 7:00 na dare zuwa 7:00 na safe.
Ya ƙara da cewa IPMAN na aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro da sauran hukumomin gwamnati domin inganta tsaro a fannin sufuri da kuma dakile satar man fetur da lodin fiye da kima, wanda ke kara ta’azzarar matsaloli a fadin ƙasar.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
