Connect with us

News

‘Yan bindiga sun sace fiye da mutum 50 a Jihar Zamfara

Published

on

yan bindiga sun sace mutane

Wasu ‘yan bindiga sun sace fiye da mutum 50 a arewa maso yammacin Nijeriya a wani gagarumin hari da ‘yan garkuwar suka kai, kamar yadda wani rahoton sa ido kan rikici da aka shirya ga Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana, wanda AFP ta gani a ranar Lahadi.

Rahoton ya ce, ‘yan bindiga sun kai hari a ƙauyen Sabon Garin Damri da ke jihar Zamfara a ranar Juma’a.

IPMAN Za Ta Hana Tankokin Mai Ɗaukar Sama Da Lita 45,000 Daga Watan Oktoba

Waɗannan ƙungiyoyin ‘yan bindiga galibi suna yin garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa, inda suke ƙwace dukiyoyin jama’ar ƙauye, kuma suna tilasta musu biyan haraji.

Rahoton ya bayyana cewa wannan shi ne karo na farko da aka samu irin wannan gagarumar satar mutane a yankin Ƙaramar Hukumar Bakura a wannan shekarar, yana mai nuna damuwa kan yadda ake samun ƙaruwar irin waɗannan hare-hare a Jihar.

 

 

Advertisement

TRT AFRIKA 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending