News
Gwamnatin Kano Za Ta Maida Gidan Yarin Kurmawa Cibiyar Tarihi Da Raya Al’adu
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana kudirinta na sauya fasalin gidan gyaran hali na Kurmawa da ke tsakiyar birnin Kano, inda za ta mayar da shi cibiyar adana tarihi da raya al’adun gargajiya na jihar.
Sanarwar hakan na kunshe ne a wani sako da Babban Mai Taimaka wa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan kafafen sada zumunta, Salisu Yahaya Hotoro, ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Asabar.
A cewarsa, gwamnati za ta kwashe dukkanin fursunonin da ke Kurmawa zuwa sabon gidan yari na Janguza, tare da mayar da tsohon ginin Kurmawa cibiyar yawon buɗe ido da ke kunshe da kayan tarihi da fasahar gargajiya.
Shi ma mai ba Gwamnan Kano shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ibrahim Adam, ya tabbatar da wannan mataki da gwamnatin ke shirin dauka, yana mai cewa:
“Gwamnatin jihar Kano zata kwashe dukkanin daurarrun dake gidan gyaran hali na Kurmawa a mayar da su Janguza, sannan za’a mayar da gidan gyaran hali na Kurmawa din ya koma gidan adana kayayyakin tarihi da raya al’adu na jihar Kano.”
-
News7 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News6 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News5 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
