Connect with us

News

Gyara Titunan Karkara Sun Fi Muhimmanci Fiye Da Na Birane — Gwamna Abdullahi Sule

Published

on

Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya bayyana cewa gyara tituna a yankunan karkara na da muhimmanci fiye da wasu tituna a birane, duba da yadda hakan ke ƙara haɗa al’umma da bunƙasa tattalin arzikin ƙananan hukumomi.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake ƙaddamar da aikin gina hanyar Wamba–Waiye–Dengi–Alizaga mai tsawon kilomita 24.5, da ke tsakanin Kananan Hukumomin Wamba da Akwanga a jihar.

‎Gawuna Ya Jinjinawa Usman Alhaji Kan Tallafa wa Karatun Yara Masu Bukata Ta Musamman ‎

An ba da kwangilar aikin, a kan kuɗin da ya kai naira biliyan 9.061, kuma ana sa ran hanyar za ta kasance muhimmin ginshiƙi wajen buɗe ƙofofin kasuwanci da sauƙaƙe zirga-zirga ga al’umma.

A yayin bikin ƙaddamarwar, Gwamna Sule ya ce: “Titunan karkara na taimakawa matuƙa wajen fitar da amfanin gona daga kauyuka zuwa kasuwanni, wanda hakan ke taimakawa wajen sauƙaƙe farashin abinci da ƙarfafa rayuwar manoma.”

Ya ƙara da cewa, “Ba gina titi kawai muke yi ba, muna ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arzikinmu ta hanyar haɗa yankunan karkara da manyan birane domin samun daidaito wajen cigaba.”

Gwamnan ya bukaci kamfanin da ke gudanar da aikin da ya bi ka’idojin injiniya da tsaro, tare da yin aikin cikin inganci da gaggawa. Haka kuma ya roƙi al’umma da su bayar da haɗin kai da kariya ga kayan aikin da ma’aikatan kamfanin.

Advertisement

“Wannan aikin wani ɓangare ne na ƙudirin gwamnatinmu na samar da ci gaban ababen more rayuwa, domin a tabbatar da cigaba ya kai ko’ina cikin jihar, ba tare da barin wata al’umma a baya ba,” in ji Gwamna Sule.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending