News
Kotu Ta Yanke Wa ƴar India Hukuncin Zaman Gidan Yari Na Shekara 5 A Kano
Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta yanke wa wata ƴar kasar India, Neetu, hukuncin dauri na shekaru biyar a gidan yari bisa kama ta da hodar iblis mai nauyin kilo 11 da aka ɓoye cikin kayan zaki.
Mai shari’a Justice Simon Amobeda ne ya yanke hukuncin a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa Neetu ta aikata laifuka guda biyu. Sai dai an ba ta zaɓin biyan tarar naira miliyan biyu maimakon zaman gidan yari.
Bello Turji Ya Saki Waɗanda Ya Yi Garkuwa Da Su Mutane 32 Ya Miƙa Makamai Bayan Shiga Tsakani
Rahotanni sun bayyana cewa Neetu ta shigo Najeriya daga Bangkok ta hanyar Vietnam da Doha, kafin a cafke ta a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano da kwayar hodar iblis ɗin.
A Lagos, wani ɗan kasuwa mai suna Ajah Johnson Uchenna da matarsa Rosemary Uchenna, an same su da laifin safarar tabar wiwi mai nauyin kilo 414.2.
Justice Deinde Dipeolu ya yanke wa Rosemary hukuncin dauri na shekaru 17 a gidan yari, yayin da mijinta Ajah ya samu hukuncin shekaru biyar da rabi, tare da zaɓin biyan tarar naira miliyan ɗaya.
Kotun ta kuma bayar da umarnin a kwace naira miliyan 3.4 daga hannunsu domin mika wa gwamnatin tarayya.
Wani ɗan Angola mai suna Mbala Dajou Abuba ya samu hukuncin shekaru biyar a gidan yari a Kano bayan da aka kama shi da kwayar cocaine mai nauyin kilo 1.8 da ya haɗiye, yayin da yake ƙoƙarin hawa jirgi zuwa birnin Istanbul na Turkiyya.
A jihar Enugu kuwa, Justice M.G. Umar ya yanke wa Eze Christian Ikenna hukuncin shekaru uku kan kowanne daga cikin laifuka biyu da aka gurfanar da shi a kai, bisa safarar cocaine mai nauyin kilo 11.2 da aka ɓoye cikin ganyen shayi.
A wani hukuncin daban da aka yanke a Lagos, Justice Ibrahim Ahmad Kala ya bayar da umarnin kwace wani otal mai dakuna 80 da kuma motocin hawa daga hannun wata ƙungiyar safarar miyagun ƙwayoyi.
Hukumar NDLEA ta bayyana cewa ta gano ƙwayar Canadian Loud mai nauyin kilo 417.3 da darajarta ta kai sama da naira biliyan ɗaya a cikin otal ɗin.
Kayayyakin da aka kwace sun haɗa da motoci irinsu Toyota Sienna, Volkswagen Van, Land Cruiser Prado, da kuma na’urorin gida kamar talabijin guda 84, injin sanyaya daki (AC) guda 70, da firiji guda 13.
