Connect with us

News

Bello Turji Ya Saki Waɗanda Ya Yi Garkuwa Da Su Mutane 32 Ya Miƙa Makamai Bayan Shiga Tsakani

Published

on

1754410415437

Shugaban gungun ‘yan bindiga da ake zargi da kai hare-hare a jihar Zamfara, Bello Turji, ya saki mutum 32 da ya yi garkuwa da su, tare da ajiye wasu daga cikin makaman sa a matsayin alamar goyon bayan zaman lafiya.

Wannan na zuwa ne bayan jerin ganawa da wasu fitattun malamai da suka hada da Sheikh Musa Yusuf Asadus-Sunnah, wanda ya jagoranci shiga tsakani a dajin Fakai, cikin Karamar Hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.

Advertisement

Yan Sanda Sun Kama Mace Bisa Zargin Satar Adai-daita Sahu a Jigawa

Sheikh Asadus-Sunnah, wanda ya bayyana hakan a wani taron addini da aka gudanar a Kaduna ranar Litinin, ya ce an gudanar da ganawar sulhu da Turji da sauran shugabannin tawagarsa sau uku a cikin watan Yuli.

“Mun gana da Bello Turji, Dan Bakkolo, Black, Kanawa da Malam Ila. Jita-jitar cewa Dan Bakkolo ya mutu ba gaskiya ba ce. Dukkansu sun amince da zaman lafiya, sun kuma mika wasu daga cikin makaman su,” in ji shi.

Advertisement

Ya ce bayan ganawar, ‘yan bindigar sun ba da damar manoma da jama’ar Shinkafi su ci gaba da zuwa gonakinsu cikin daji ba tare da fargaba ba. Haka zalika, an yi yarjejeniya cewa Fulani za su iya shiga cikin gari ba tare da tsangwama daga masu sa kai ba.

A cewar Sheikh Yusuf, mutanen da Turji ya sako sun hada da mata da yara da suka kwashe kusan wata hudu a hannun ‘yan bindigar. Wasu daga cikinsu sun fuskanci mawuyacin hali, inda aka samu mace guda da ta haihu a daji, sannan wata kuma ta kamu da cizon maciji.

Advertisement

Malamin ya ce tun bayan yarjejeniyar, an fara samun sauyin yanayi a yankin Shinkafi, inda mutane ke ci gaba da aikin gona cikin kwanciyar hankali.

Duk da irin wannan ci gaba, malamin ya ce ba su bukaci Bello Turji ya mika dukkan makaman sa ba, domin hakan na iya janyo farmaki daga wasu kungiyoyin makiyaya da ke da sabani da shi.

Advertisement

Ya kuma gargadi wasu malamai da ke amfani da kafafen sada zumunta suna sukar Turji, yana mai cewa hakan zai iya janyo rikici fiye da alheri.

“Shekaru da dama ana kashe mutane, amma yanzu da aka samu wannan dama ta sulhu, ya kamata a yi amfani da ita,” in ji shi.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

PREMIUM TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending