News
Hukumomi Sun ƙayyade N20,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Sadaki A Kano
Hukumar Zakka da Hubusi ta jihar Kano, tare da haɗin gwiwar Hukumar Shari’a, Majalisar Malamai, Ƙungiyar Limaman Masallatan Juma’a da kuma Ƙungiyar Ma’aikatan Zakka da Wakafi ta Ƙasa, sun amince da sabbin ƙa’idoji da suka shafi nisabin zakka, diyya da kuma sadakin aure a jihar.
A taron da aka gudanar a Kano ranar Alhamis, mahalarta taron sun yanke shawarar amincewa da Naira dubu 20 a matsayin mafi ƙarancin sadakin aure, Naira miliyan 150 a matsayin diyya ga wanda aka kashe bisa kuskure, da kuma Naira dubu 985 a matsayin nisabin zakka bisa lissafin farashin Durham.
Zaben Cike Gurbi: DSS Ta Cafke Wani Wakilin Jam’iyya Da N30m Bisa Zargin Siyan Kuri’u A Kaduna
Babban Sakataren Ƙungiyar Ma’aikatan Zakka da Wakafi ta Ƙasa, Farfesa Aliyu Dahiru Muhammad daga Jami’ar Bayero Kano, ya bayyana cewa an kuma yanke hukuncin ci gaba da gudanar da irin wannan zama duk bayan watanni uku domin duba da kuma sabunta ƙa’idojin da aka cimma.
Ya ce: “Hukumar da sauran abokan hulɗa za su ci gaba da tattaunawa a kai a kai domin tabbatar da cewa waɗannan ƙa’idoji suna tafiya daidai da yanayin tattalin arziki da halin rayuwar al’umma.”
A cewarsa, za a sanar da gwamnatin jihar domin shirya taron wayar da kai da kuma haɗa kai da manema labarai wajen isar da saƙon ga jama’a ta hanyoyin da suka dace.
