News
Zaben Cike Gurbi: DSS Ta Cafke Wani Wakilin Jam’iyya Da N30m Bisa Zargin Siyan Kuri’u A Kaduna
Jami’an tsaro sun cafke wani da ake zargin wakilin jam’iyya dauke da fiye da naira miliyan 25.9 a zahiri, wanda ake kyautata zaton an ware don karkatar da kuri’un zaben cike gurbi da za a gudanar a ranar Asabar a Jihar Kaduna.
LEADERSHIP ta rawaito cewa wanda ake zargin, mai suna Shehu Aliyu Patangi, an kama shi ne da misalin karfe 3:30 na asuba ranar Asabar a wani shahararren otel da ke kan titin Turunku, cikin garin Kaduna, ta hannun jami’an ‘yansanda tare da na hukumar tsaro ta DSS da sauran hukumomin tsaro.
Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, a cikin wata sanarwa ranar Asabar, ya bayyana cewa an gano jimillar kudi har ₦25,963,000 a wurin wanda ake zargin, wanda ake tunanin an tanada domin sayen kuri’un masu zabe a mazabar Chikun/Kajuru.
DSP Hassan ya kara da cewa yayin bincike, Patangi ya amsa cewa kudin an tanade su ne domin cinikayya da masu zabe, inda kuma ya roki a yi masa sassauci.
