News
Gidauniyar Dr Aminu Magashi Ta Raba Magungunan Naira Dubu Dari Biyu A Asibitin Murtala
Gidauniyar Dr Aminu Magashi Garba (AMG) tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyi masu zaman kansu – Kano State Health Care Forum, Amkas, da Yospis – ta mika tallafin magunguna da darajarsu ta kai kimanin naira Dubu Dari biyu 200 a Asibitin Koyarwa na Murtala Muhammad da ke Kano.
Tallafin, wanda aka mika a cikin makon nan, na nufin tallafawa marasa galihu da ke fama da rashin lafiya a asibitin, tare da inganta harkokin kiwon lafiya a jihar.
Hatsarin Mota Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 12 Tare Da Jikkata 5 A Kano
Shugaban gidauniyar, Dr Aminu Magashi Garba, ya ce wannan shiri zai ɗauki tsawon shekara guda, inda za a rika raba magunguna ga manyan asibitoci da kananan cibiyoyin kiwon lafiya a unguwanni daban-daban na Kano. Ya kara da cewa, za su mayar da hankali wajen taimaka wa sashen kula da mata masu juna biyu, domin rage radadin haihuwa da kuma matsalolin lafiya .
“Mun himmatu wajen tabbatar da cewa marasa galihu suna samun magungunan da suka dace a kan lokaci, musamman a manyan asibitoci da kuma kananan asibitocin yankuna,” in ji Dr Magashi.
Shi kuwa Shugaban Asibitin Murtala Muhammad, Dr Hussaini Muhammad, ya bayyana jin dadin su kan wannan tallafi, yana mai cewa zai taimaka matuka wajen kula da marasa lafiya da ake kawo musu sakamakon haɗurra da kuma masu fama da cututtuka daban-daban.
“Za mu tabbatar an yi amfani da magungunan bisa yadda ya kamata, domin su amfanar da wadanda aka yi niyya,” in ji Dr Hussaini.
