Connect with us

News

Lagos Ta Dare Kan Teburin Birane Mafi Cunkoson Ababen Hawa A Duniya A 2025 — Rahoton Numbeo

Published

on

Lagos state

Wani rahoto da cibiyar tattara bayanai ta Numbeo ta fitar ya bayyana cewa Lagos ce birni mafi fama da cunkoson ababen hawa a duniya a shekarar 2025, inda ta zarce wasu fitattun birane da suka shahara da irin wannan matsala kamar Los Angeles ta Amurka, New Delhi ta Indiya da kuma San Jose ta Costa Rica.

Rahoton ya nuna cewa matafiya a Lagos kan shafe akalla mintuna 70 a tafiya guda ɗaya, lamarin da ke nuna tsananin matsalar zirga-zirga a birnin.

Advertisement

‎ Jam’iyyar APC Ta Buƙaci A Soke Zaɓen Cike Gurbi A Kano

Numbeo ta ce wannan bincike ya samo asali ne daga bayanan da jama’a suka bayar kai tsaye, ba daga hukumomin gwamnati ba. An haɗa da tsawon lokacin tafiya, jin daɗin matafiya, gurbatar muhalli da kuma ingancin tsarin sufuri.

A jerin da aka fitar, San Jose ta Costa Rica ta zo na biyu inda ake shafe mintuna 63 a tafiya ɗaya. Los Angeles ta zo a na uku, sai Sharjah a Hadaddiyar Daular Larabawa a na hudu, yayin da Colombo ta Sri Lanka ta zo a matsayi na biyar.

Advertisement

A ƙasa da su akwai Delhi (Indiya) da ta zo na shida, Dhaka (Bangladesh) a na bakwai, sai Kolkata (Indiya), Guatemala City (Guatemala) da Mexico City (Mexico) suka cika jerin goma na farko.

Sai dai duk da wannan matsala, gwamnatin jihar Lagos ta ce tana ƙoƙarin rage cunkoso ta hanyar inganta harkokin sufuri. Cikin matakan da aka ɗauka akwai Blue Line Metro Rail da aka kaddamar a 2023, mai tsawon kilomita 13 daga Marina zuwa Mile 2, wadda tuni ta jigilar miliyoyin fasinjoji. Ana ci gaba da aikin tsawaita layin zuwa Okokomaiko, wanda ake sa ran kammala shi a 2026.

Advertisement

Haka kuma, Red Line Rail mai tsawon kilomita 37 ta fara aiki a 2024. Matakin farko daga Agbado zuwa Oyingbo (kilomita 27 da tashoshi takwas) ya riga ya fara rage cunkoson ababen hawa a wasu manyan wurare na birnin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending