Connect with us

Labarai

2027: Usman Alhaji Ya Bukaci Matasa Su Yi Rijistar Katin Zaɓe Domain Zaɓar Shugabanni Nagari

Published

on

IMG 20250618 WA0029
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Tsohon Sakataren Gwamnatin Kano, Alhaji Usman Alhaji, ya bukaci matasa da duk wanda ya kai shekaru 18 da haihuwa da su tabbata sun yi rijistar katin zaɓe kafin babban zaɓen 2027.

Ya yi wannan kira ne a lokacin taron manema labarai da aka shirya a Kano karkashin ƙungiyar Volunteers for Democracy, inda ya ce wajibi ne ‘yan ƙasa su yi amfani da damar kada kuri’a wajen zaɓar shugabanni nagari.

Yadda Manoma Ke Korafin Tafka Asara Sakamakon Faduwar Farashin Kayan Abinci A Najeriya

Alhaji Usman, wanda shi ne shugaban  ƙungiyar, ya ce manufar Volunteers for Democracy ita ce wayar da kan jama’a kan muhimmancin mulki nagari da kuma bin doka.

“Kada kuri’a shi ne hanya ta doka da zai tabbatar da dimokuraɗiyya mai inganci. Muna kira ga duk wanda ya kai shekaru 18 da ya garzaya cibiyar rijista mafi kusa domin samun katin zaɓensa,” in ji shi.

Ya kuma bayyana cewa ƙungiyar ta fara rijistar mambobi ta yanar gizo da ta hannu a kananan hukumomi 44 na Kano, inda ake sa ran daga mutum 60,000 da ake da su a yanzu za a kai 200,000 kafin ƙarshen 2025.

A cewarsa, kowace siyasa tana da nata yanayi, kuma yanzu tuni aka fara jan layin siyasa kafin zaɓen 2027. Ya gargadi jama’a musamman mambobin ƙungiyar da su kauce wa yaudara daga jam’iyyun adawa tare da tantance bayanai a kafofin sada zumunta.

Advertisement

Daga ƙarshe, Alhaji Usman ya yi addu’o’i ga fitattun mutanen da suka rasu kwanan nan, ciki har da tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, attajiri Alhaji Aminu Alhassan Dantata, da Sarkin Zuru, Janar Sani Sami (ritaya).

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending