News
Yadda Manoma Ke Korafin Tafka Asara Sakamakon Faduwar Farashin Kayan Abinci A Najeriya
Manoma a sassa daban-daban na Najeriya na ci gaba da kukan tafka asara duk da faduwar farashin kayan abinci a kasuwanni, lamarin da ke jefa su cikin damuwa da rashin samun riba.
Rahotanni daga Kano, Kaduna da Yobe sun nuna cewa manoma na tilasta sayar da amfanin gonarsu a farashi mai rahusa, duk da tsadar kuɗin da suka kashe wajen shuka da sarrafa gona.
Hisbah Ta Kama Mutum 62 Da Ake Zargi Da Aikata Badala A Kano
A jihar Yobe, wani manomi, Muhammad Muhammed Zaridin, ya shaida cewa:
> “A bana mun kashe kuɗi fiye da yadda muka kashe a bara wajen noma, amma yanzu farashin hatsi ya yi ƙasa. Ko da yake a matsayimmu na manoma muna farin cikin ganin abinci ya yi sauƙi a kasuwa, amma rashin sauƙin kayan noma kamar taki da magungunan feshi shi ne babban abin da ke damunmu. Wannan ne ya sa muka shiga asara.”
Ya ƙara da cewa, musamman ma shinkafa daga jihar Yobe ta fadi ƙwarai, inda ake siyar da buhu a kan N50,000 a bara, amma yanzu bai wuce N30,000 zuwa N35,000 ba.
“Yanayin tsadar kayan aiki da kuɗin da aka kashe wajen noma shi ke sa manoma shiga asara. Wani lokaci rashin yin noma ma ya fi, domin a yau ana yin noma ne domin samun riba, ba wai kawai mutum ya wahala babu abin da zai ci ba,” in ji shi.
Haka nan a Kaduna, wani manomi, Salim Bashir, ya bayyana cewa buhun masara da aka saba sayarwa a sama da N50,000 a bara yanzu bai wuce N30,000 ba. Shinkafa da gero suma sun yi ƙasa ƙwarai.
“Mun yi wahala wajen noma, mun kashe kuɗi wajen shuka da sarrafa gona, amma yanzu ga amfanin gona a hannunmu babu masu siya sosai saboda rashin kuɗi a hannun jama’a,” in ji shi.
A Kano kuwa, wasu manoma sun koka da cewa rashin kayan ajiya da hanyoyin adanawa na zamani ya tilasta musu siyar da amfanin gona cikin gaggawa a farashi mara riba.
Masani a fannin noma, Auwal Sadeeq Belu, ya yi gargadin cewa wannan yanayi na iya jawo koma-baya a shekara mai zuwa, domin manoma za su rage sha’awar yin noma idan suka kasa cin moriyar amfanin gonarsu. Ya yi kira ga gwamnati da ta samar da tallafi, kayan ajiya na zamani da kuma sauƙaƙe musu hanyoyin samun kuɗi.
Sai dai duk da faduwar farashin kayan abinci, masu sharhi sun nuna cewa tsadar rayuwa da ƙarancin kuɗin shiga na hana jama’a cin moriyar rahusar abincin a Najeriya.
