News
Hisbah Ta Kama Mutum 62 Da Ake Zargi Da Aikata Badala A Kano
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce jami’anta sun kama mutum 62 da ake zargi da aikata badala a makarantar koyon sana’o’i ta NITT da ke ƙaramar hukumar Dawakin Kudu, Kano.
Jami’an hukumar sun ce samamen ya gudana ne a ranar Lahadi bayan samun bayanan sirri daga al’umma.
Jami’an NDLEA Sun Cafke Babban Mai Safarar Ƙwayoyi , Ta Lalata Wiwi Sama Da Kilo Dubu 37
Mataimakin Babban Kwamandan hukumar, Dakta Mujahideen Abubakar, ya tabbatar da kamen ga Jaridar INDA RANKA ,Daga cikin waɗanda aka kama akwai maza 27 da mata 35, inda aka same su cikin wani taro da ake alakantawa da ayyukan badala.
“Mun samu nasarar kama su ne bayan samun ƙorafe-ƙorafe daga al’umma. Yanzu haka suna hannunmu, kuma za a ci gaba da bincike kafin ɗaukar matakin da ya dace,” in ji hukumar.
Hisbah ta ce da zarar an kammala bincike za a gurfanar da su a gaban kotu domin ɗaukar matakina doka.
