News
Jami’an NDLEA Sun Cafke Babban Mai Safarar Ƙwayoyi , Ta Lalata Wiwi Sama Da Kilo Dubu 37
Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta cafke wani sanannen mai safarar miyagun ƙwayoyi, Sunday Ibigide, tare da abokin harkallarsa Clement Osuya a Asaba, jihar Delta.
Rahoton hukumar ya bayyana cewa an kama su ne da ƙunshin ƙwayar skunk 250 mai nauyin kilo 138, a cikin wata mota da suka tanada domin rabawa dillalan su.
Dalilan Ayyana Zaɓen Cike Gurbi A Zamfara A Matsayin Wanda Bai Kammala Ba —INEC
Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi, ya ce an shafe sama da shekaru uku ana neman Ibigide tun bayan da aka gano hannunsa a wata harkalla a ranar 19 ga Maris, 2022, inda aka kama kilo 24.137 na ƙwayoyi.
Ya ƙara da cewa NDLEA ta gudanar da bincike mai zurfi a jihohi daban-daban, wanda ya kai ga cafke masu hannu da yawa a safarar miyagun ƙwayoyi.
A wani samame da jami’an NDLEA tare da haɗin gwiwar sojoji da ’yan banga suka kai a Enugu Ezike, Jihar Enugu, an gano da kuma lalata kimanin kilo dubu 37,500 na wiwi a gonaki masu fadin hektoci 15.
Babafemi ya ce a yayin wannan samame an kama mutane shida da ake zargi da hannu a cikin haramtacciyar harka.
Masu hannu a wannan harkalla sun haɗa da ,Ugwuanyi Chinaso (23), James Negedu (26), Sopuruchukwu Obido (22), Ebuka Onu (30), Ukwueze Sunday (42) da Oguche Friday.
Hukumar ta ce an kuma kwato ƙarin kilo 74.5 na miyagun ƙwayoyi, kuma za a gurfanar da su a kotu.
-
News23 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
