News
Najeriya: Harajin Mai Sabuwar Hanyar Bunƙasa Ƙasa Ko Cinye Dukiyar Kasa?
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ba za ta janye kudirin ƙara haraji kan man fetur ba, duk da adawar da ƙungiyoyin ƙwadago ke yi.
Gwamnatin ta ce sabon harajin ya zama wajibi wajen samar da kuɗaɗen da za a yi amfani da su wajen gina hanyoyi da sauran muhimman ayyukan more rayuwa.
Sai dai ƙungiyar ƙwadago ta TUC ta bai wa gwamnati wa’adin makonni biyu ta janye kudirin, ko kuma ta fuskanci matakai masu tsauri daga ma’aikata.
Abin da gwamnati ke cewa
Shugaban kwamitin gyaran tsarin haraji na tarayya, Taiwo Ayodele, ya ce:
“Wannan haraji ba sabon abu ba ne. Sama da ƙasashe 150 na duniya suna amfani da shi. Idan hanyoyi sun inganta, zirga-zirga za ta kasance cikin sauƙi, hatsari zai ragu, kuma kuɗin gyaran motoci zai sauka.”
Ya ce a Ghana akwai haraji sama da guda shida a harkar man fetur, sannan a Afirka ta Kudu ana kashe harajin da ya kai kashi 30 cikin 100 daga farashin mai wajen gyara hanyoyi.
Abin yan ƙwadago ke cewa
Sai dai ƙungiyar ƙwadago ta TUC ta ce sabon kudirin ba komai ba ne illa ƙarin nauyi ga jama’a.
Sakataren ƙungiyar, Dakta Abbayo Nuhu, ya ce “Ko dai gwamnati ta sake neman amfani da dukiyar talakawa wajen cin gajiyar ’yan tsiraru, ko kuma ta fuskanci adawa daga al’umma.”
Masana tattalin arziki na gargadi
Wani masani kan tattalin arziki, Dakta Isa Abdullahi, ya ce halin da ƙasar ke ciki bai dace da ƙarin matsin rayuwa kan jama’a ba.
Ya tunatar da yadda gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ta rushe wasu cibiyoyin hanyoyi a 2004 saboda zargin wawaso da dukiyar jama’a, wanda ya jawo lalacewar fiye da kashi 70 cikin 100 na hanyoyin ƙasar.
Tambaya ta rage
Shin sabon harajin zai zama hanyar bunƙasa tattalin arziki da inganta hanyoyi, ko kuwa wata dabarace ta sake cinye dukiyar jama’a?
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
