Connect with us

News

Ƙungiyar Likitoci Sun Bai Wa Gwamnatin Tarayya Sa’o’i 24 Kafin Tsunduma Yajin Aiki

Published

on

Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta Najeriya (NARD), ta bai wa Gwamnatin Tarayya sa’o’i 24 domin ta aiwatar da bukatunsu, in ba haka ba za su tsunduma yajin aiki daga ranar Juma’a.

Wannan gargadi na zuwa ne bayan cikar wa’adin kwanaki 10 da ƙungiyar ta bayar a baya, inda ta yi korafi kan rashin biyan hakkokin mambobinta.

Advertisement

Najeriya: Harajin Mai Sabuwar Hanyar  Bunƙasa Ƙasa Ko Cinye Dukiyar Kasa?

Likitocin – waɗanda galibinsu ke aiki a asibitocin koyarwa da na ƙwararru – sun dade suna gudanar da yajin aiki lokaci zuwa lokaci saboda matsalolin rashin biyan kuɗaɗen su.

A cikin sabbin bukatunsu, likitocin sun nemi a biya musu kuɗin horon shekarar 2025, bashin albashi da sauran alawus-alawus da suka tara. Haka kuma sun roƙi gwamnati ta amince da takardar shaidar digirin West African postgraduate, tare da warware matsalolin da suka shafi walwalar mambobinsu a Jihar Kaduna da kuma Asibitin Koyarwa na LAUTECH, Ogbomoso.

Advertisement

Shugaban ƙungiyar, Dokta Tope Osundara, ya bayyana cewa an yanke wannan matsaya ne bayan taron awanni shida na kwamitin gudanarwar ƙasa da suka gudanar ta intanet.

Ya ce gwamnati ta riga ta yi wasu alƙawura kan bukatun likitocin, amma har yanzu ba ta ɗauki matakin aiwatar da su ba.

Advertisement

“Idan gwamnati ba ta ɗauki wani mataki cikin sa’o’i 24 ba, za mu fara yajin aiki daga ranar Juma’a,” in ji shi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending