Connect with us

News

Budurwar  Da Ta Auri Kanta Ta Nemi Saki Bayan Shekara Ɗaya

Published

on

image 122

Wata ‘yar asalin Brazil mai suna Suellen Carey, wacce ke zaune a London, ta nemi saki daga aurenta da kanta bayan shekara guda da ɗaurin auren.

Carey mai shekaru 36, ta yi suna a bara bayan ta daura aure da kanta a wani biki da ta kira “sologamy”, lamarin da ya ja hankalin kafofin watsa labarai na duniya. Ta kuma yada hotuna da bidiyon bikin ga mabiya sama da 400,000 a shafinta na Instagram.

An Gurfanar Da Matashi A Kotu Bisa Zargin Fasa Shago Da Satar Kayayyakin Gyaran Waya

Sai dai duk da ƙoƙarinta na ganin dangantakar ta dore, ciki har da zuwa zaman shawarwari ita kaɗai, Carey ta ce ta gaji da matsin lamba da take yi wa kanta. Ta yi zaman counselling sau 10, amma daga ƙarshe ta fahimci cewa kawo ƙarshen aurenta shi ne mafi alheri gare ta.

A cewarta, aurar da kanta ya taimaka mata wajen gano kanta da samun waraka, amma daga baya ta fahimci cewa ci gaban rayuwa ya buƙaci ta rungumi sabon mataki.

Suellen ta ce yanzu ta shirya shiga sabon babi na rayuwa, tana kuma buɗe zuciyarta don wata alaka ta zahiri. Ta ce: “Lokaci ya yi na ci gaba, kuma na shirya buɗe zuciyata don samun abokin rayuwa na hakika.”

 

Advertisement

 

VANGUARD

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending