Connect with us

News

An Gurfanar Da Matashi A Kotu Bisa Zargin Fasa Shago Da Satar Kayayyakin Gyaran Waya

Published

on

Kotu

Wata babbar kotun majistare da ke Ado-Ekiti ta gurfanar da wani matashi mai shekaru 25, Ojo Samuel, bisa zargin fasa shago da kuma satar kayayyakin wayar hannu da kimarsu ta kai Naira miliyan 1.4.

Mai gabatar da ƙara, Insfekta Olasunkanmi Bamikole, ya shaida wa kotu cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 1 ga Maris, 2025, a unguwar Osekita da ke Iworoko-Ekiti, inda ya shiga shagon wani mai suna Sunday Peter.

Advertisement

Bankin Ya Kori Ma’aikaciyarsa Daga Aiki Sannan Ya Maye Gurbinta Da AI Da Ta Horas Da Shi Aiki

A cewar Bamikole, Samuel ya kwashe kayan wayar hannu ciki har da screen guard da pouch, abin da ya sabawa dokokin laifuka na Jihar Ekiti na shekarar 2021.

Sai dai wanda ake tuhuma ya musanta zargin, yayin da lauyansa, Gbenga Ariyibi, ya roƙi kotu ta ba shi beli bisa alkawarin cewa ba zai tsere wa shari’a ba.

Advertisement

Alkalin kotun, Adefunke Anoma, ta bayar da belin kudi N100,000 ga wanda ake tuhuma tare da shaidu biyu masu matsayin ma’aikata a mataki na 14 a gwamnati da kuma gabatar da takardun mallakar fili.

An dage shari’ar zuwa ranar 9 ga Oktoba, 2025, domin ci gaba da saurare.

Advertisement

 

THE PEOPLES GAZETTE

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending