News
Mauludi Ba Wurin Hayaniya Ba Ne, Wurin Natsuwa Da Ladabi Ne – Sheikh Ibrahim Khalil”
Shugaban Majalisar Shura ta Malamai a jihar Kano, Sheikh Malam Ibrahim Khalil, ya ce wajibi ne a gudanar da tarukan Mauludi cikin natsuwa da ladabi, kasancewar ana ambaton Allah da ManzonSa (S.A.W) a irin wannan lokaci.
Sheikh Khalil ya bayyana haka ne a lokacin da ya halarci Mauludin Annabi (S.A.W) da Mahmud Sa’id Adahama ke shirya a kowace shekara a gidansa da ke Nasarawa GRA, Kano.
Ya ce kyautatawa da taimako na daga cikin manyan dabi’un Manzon Allah (S.A.W), kuma hakan na taimaka wajen rage radadin talauci da gina al’umma mai kwanciyar hankali. Malamin ya kuma yabawa masu shirya irin wannan taro da nufin kara karfafa soyayya ga Manzon Allah.
“Ya kamata wajen Mauludi Annabi (S.A.W) ya kasance cikin nutsuwa da ladabi. Rashin yin hakan rashin girmamawa ne ga Maulidin da kuma ga Manzon Allah,” in ji Sheikh Khalil.
A nasa bangaren, Mahmud Adahama ya ce wannan shekarar ta Mauludi ta kasance ta musamman, saboda ta zo daidai da cikar shekaru 1,500 da haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W). Ya ce soyayyar Manzon Allah ce ta sanya shi ci gaba da shirya taron duk shekara.
Adahama ya kuma yi kira ga masu hali da su tallafa wa al’umma, musamman marasa karfi, domin rage musu radadin rayuwa.
Taron ya samu halartar manyan malamai da fitattun mutane daga ciki da wajen jihar Kano, inda aka rufe shi da addu’o’in samun zaman lafiya a Kano da Najeriya baki daya.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
