News
Kotu Ta Yanke Wa Uwa Da Uba Hukuncin Shekaru 14 A Gidan Yari Saboda Mutuwar Jaririyarsu
Wata kotu a Birtaniya ta yanke wa wata mata ’yar gidan masu kudi, Constance Marten, tare da saurayinta Mark Gordon, hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari bayan an same su da laifin kisan kuskure na jaririyarsu Victoria.
Rahotanni sun ce Marten da Gordon sun tsere da jaririyar ce domin kauce wa a kwace ta daga hannunsu, abin da ya tayar da hankulan jama’a a fadin kasar, inda aka kashe sama da fam miliyan 1.2 wajen gudanar da bincike da neman su.
Mauludi Ba Wurin Hayaniya Ba Ne, Wurin Natsuwa Da Ladabi Ne – Sheikh Ibrahim Khalil”
Tun kafin wannan lamari, hukumomi sun riga sun kwace sauran ’ya’yansu hudu saboda barazanar da ake ganin lafiyarsu ke ciki. Sai dai daga bisani, ma’auratan suka dauki jaririyar suka zauna a wani sansani cikin sanyi mai tsanani, lamarin da ya janyo mutuwarta.
A lokacin da ake karanta hukuncin, Marten mai shekara 38 ta yi dogon numfashi, yayin da Gordon mai shekara 51 ya zauna yana kallon gaba. Alkalin kotun ya kara da cewa Gordon zai yi karin shekaru hudu a gidan yari saboda hadarin da yake iya haifarwa ga al’umma.
Sai dai duka biyun za su yi kusan kashi biyu bisa uku na wa’adin da aka yanke musu kafin a sake su.
Tun a watan Yuli aka tabbatar da cewa sun aikata laifuka da suka hada da kisan kai ta hanyar sakaci mai tsanani, cin zarafin yaro, ɓoye haihuwa da kuma karkatar da shari’a.
Shari’ar ta dauki kusan shekaru biyu tana gudana, inda aka kashe sama da fam miliyan 2.8 daga kudaden haraji wajen gudanar da ita.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
