News
Akalla Mutum 7 Sun Jikkata Bayan Da Manyan Motoci Guda Biyu Kayi Karo
Akalla mutum bakwai sun jikkata bayan manyan motoci guda biyu sun yi karo a yankin Arinkinkin, Agric, da ke Ogbomosho a jihar Oyo.
Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta jihar, Morouf Akinwande, ya ce lamarin ya faru da misalin karfe 1:15 na rana a ranar Litinin.
An Gurfanar Da Matashi Mai Shekaru 31 A Kotu Bisa Zargin Satar Wayar iPhone
Ya bayyana cewa wata mota da ke dauke da sinadarai ce ta kama da wuta bayan hadarin, sai dai jami’an kashe gobara karkashin jagorancin CFM Oladejo Kola sun dakile gobarar daga bazuwa zuwa wata motar da ke dauke da hatsi.
Akinwande ya ce an kai mutum bakwai da suka samu raunuka zuwa Asibitin Bowen Teaching Hospital da ke Ogbomosho domin kulawar gaggawa, yayin da aka dawo da zirga-zirgar ababen hawa yadda aka saba
