Connect with us

News

An Gurfanar Da Matashi Mai Shekaru 31 A Kotu Bisa Zargin Satar Wayar iPhone

Published

on

Rundunar ‘yan sanda ta gurfanar da wani matashi mai shekaru 31, Patrick Amobi, a gaban kotun majistare da ke Iyaganku, Ibadan, bisa zargin satar wayar iPhone mallakar wata mata.

Mai gabatar da ƙara, Insifekta Adeshina Folaranmi, ya shaida wa kotu cewa Amobi tare da wasu da suka tsere sun saci wayar iPhone mai darajar N300,000, mallakar Dolapo Nwanya, a unguwar Apata, ranar 24 ga watan Agusta.

DSS Ta Maka Sowore, Meta Da X A Kotu

Amobi ya musanta laifin a gaban kotu, inda aka tuhume shi da haɗa baki da sata.

Alkalin kotun, Oluwabusayo Osho, ta bayar da belinsa kan kudi N200,000 tare da mutane biyu da za su tsaya masa.

An dage shari’ar zuwa ranar 29 ga watan Disamba domin ci gaba da saurare.‎

 

Advertisement

 

NAN 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending