News
DSS Ta Maka Sowore, Meta Da X A Kotu
Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta shigar da kara a kotun tarayya da ke Abuja kan dan gwagwarmaya kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore.
A cikin karar, hukumar ta kuma hada kamfanin X Corp., masu kula da manhajar X, da Meta Platforms Inc., wato masu kula da Facebook, a matsayin wadanda ake kara tare da shi.
Cizon Macizai Ya Lakume Rayukan Mutane 23, Sama Da 1,800 Sun Samu Rauni A Gombe — Rahoto
A takardun da aka shigar a ranar 16 ga Satumba, 2025, DSS ta bayyana cewa Sowore ya bata sunan shugaban kasa Bola Tinubu, inda ta ce ya wallafa sakonni a shafukan sada zumunta inda ya kira shi “barawo”.
An ce rubutun da ake magana a kai an wallafa su ne a ranar 25 da 26 ga watan Agusta, lokacin da shugaban kasar ya ke ziyarar aiki a Brazil.
Sai dai har yanzu ba a bai wa shari’ar alƙali ba, kuma babu ranar da aka saka domin gurfanar da Soworea kotu.
