Connect with us

News

Jama’a Sun fi Yadda Da Neman Magani A Shagunan Chemist Fiye Da Zuwa Asibiti Domin Ganin Likita

Published

on

images (2)

Rahotanni sun nuna cewa mutane da dama na fi karkata zuwa shagunan sayar da magunguna na bakin titi, wato Chemist, wajen neman magani maimakon zuwa asibitoci domin ganin likita a Najeriya

Wasu daga cikin mutanen da Jaridar Inda Ranka ta yi hira da su sun bayyana cewa rashin kudi, tsadar magani a asibiti da kuma wahalar jira su ne manyan dalilan da ke tilasta musu wannan dabi’a.

Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya,

Khadija Nasser, mazauniyyar Kano, ta ce “Idan na shiga shagon magani, cikin ‘yan mintuna zan samu abin da nake nema. Amma a asibiti sai an tsaya ana bata lokaci, wani lokaci ma ba a kula da marasa lafiya yadda ya kamata.”

Haka zalika, Salim Bashir, wani dan kasuwa, ya ce saboda rashin lokacin zaman asibiti, shi yasa yake zuwa shagon magani domin samun magani cikin sauri.

Sai dai masana lafiya sun gargadi cewa wannan dabi’a na iya jefa rayukan jama’a cikin hadari, domin ba a sha magani ba tare da kulawar likita ba.

Wani likita daga jihar Adamawa ya ce “Shagunan magani ba za su maye gurbin asibiti ba. Mutane suna cutar da kansu da irin wannan dabi’a.”

Advertisement

Dr. Zarima Saleh Yusuf daga Asibitin Koyarwa na Modibbo Adama, Yola, ya ce mafi yawan mutanen da ke rarraba magani a shagunan bakin titi ba kwararru ba ne.

“Ba su da kwarewa kamar yadda likitoci da ma’aikatan lafiya a asibitoci suke da ita,” in ji shi kamar yanda ya bayyanawa FRI HAUSA 

Masu lura da harkokin lafiya sun bukaci gwamnati da ta dauki tsauraran matakai tare da wayar da kan jama’a domin kare lafiyar al’umma.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending