News
Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya,
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, Rt. Hon. Haruna Aliyu Dangyatin, ya tsallake rijiya da baya a ranar Litinin, bayan da ayarinsa suka gamu da mummunan hatsari a kan hanyar zuwa karamar hukumar Maigatari na jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa Kakakin Majalisar na kan hanyarsa ne domin halartar wani gangamin siyasa da aka shirya a karkashin shirin “Dandalin Tattaunawar Gwamnati da Jama’a” lokacin da lamarin ya faru.
Wani ganau ya shaida wa manema labarai cewa ɗaya daga cikin motocin ayarin, mota kirar Toyota Hilux ɗauke da jami’an ‘yansanda, ta kwace a hanya, inda ta yi ta hantsalawa kafin ta tsaya. Ya ƙara da cewa sauran motocin ayarin, ciki har da wacce Kakakin Majalisar ke ciki, sun yi nasarar tsayawa a daidai lokaci.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa an garzaya da jami’an ‘yansandan da suka ji raunuka zuwa babban asibitin Gumel. An ce sun farfaɗo daga suma bayan samun kulawar gaggawa.
