Connect with us

News

Gwamantin Kano Ta Kammala Tsarin Ayyukan Lafiya Na 2026

Published

on

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano tare da hadin gwiwar hukumomi da abokan ci gaba ta kammala taron kwana hudu domin tsara aikin lafiya na shekara ta 2026 (AOP).

‎An gudanar da taron ne a otal din Pyramid da ke Kaduna daga ranar 11 zuwa 15 ga Satumba, 2025, inda aka tattauna yadda za a daidaita tsare-tsaren lafiya domin inganta ayyukan kiwon lafiya a jihar.

Abdullahi Abbas Ya Yaba Wa Baffa Babba Dan Agundi Kan Tallafa Wa Matasan APC A Kano

‎Shirin AOP na 2026 ya yi daidai da bukatun lafiyar Kano, kuma ya dace da tsarin Health Sector Strategic Blueprint (HSSB), shirin Nigeria Health Sector Renewal Investment Initiative (NHSRII) da kuma HOPE Project.

‎Taron ya samu halartar Kwamishinan Lafiya na Kano (wakilcin Darakta Janar na PHCMB), Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Kano, wasu shugabannin kwamitoci na majalisar, da Sakataren Dindindin na ma’aikatar. Haka kuma shugabannin hukumomi kamar PHIMA, HMB, KSACA, KHETFUND, KSCHMA, DMCSA da KNCDC sun halarta. Kungiyoyin fararen hula da abokan ci gaba irin su WHO, UNICEF, FCDO Lafiya da SANDHDEF.

‎A taron, mahalarta sun duba ayyuka da alamu na tsari, suka gano inda ake maimaitawa, sannan suka daidaita shirin hukumomi daban-daban zuwa tsari guda na jihar. An kafa kwamiti da zai rika bibiyar yadda ake aiwatar da ayyuka bisa Disbursement Linked Indicators (DLIs).

‎Daga cikin kudurorin da aka cimma akwai neman karin hanyoyin samun kudade, ware wa hukumomi nauyin DLIs domin karin gaskiya, tabbatar da ayyuka sun yi daidai da binciken halin da ake ciki (SITAN), da kuma tabbatar da cewa dukkan ayyuka sun zama SMART (Specific, Measurable, Achievable, Realistic, Time-bound).

Advertisement

 

‎Kwamishinan Lafiya na Kano, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ya gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa goyon bayan da yake baiwa bangaren lafiya. Haka kuma ya jinjinawa majalisar dokokin jihar, shugabannin hukumomi, kungiyoyin fararen hula da abokan ci gaba kan gudummawar da suka bayar wajen nasarar shirin.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending