Labarai
FUDMA Ta Yi Bikin Kaddamar Da Dalibai 1,000 Da Sanata Barau Ya Dauki Nauyin Karatunsu

Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA), a Jihar Katsina, ta gudanar da bikin kaddamar da dalibai 1,000 da suka samu tallafin karatun digiri daga shirin tallafin ilimi na Sanata Barau I. Jibrin, CFR, FCNA, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.
Bikin ya gudana a harabar jami’ar ranar Litinin tare da halartar manyan baki, ciki har da Shugaban Hukumar Ci gaban Arewa maso Yamma (NWDC), Farfesa Abdullahi Shehu Maaji; Shugaban Ma’aikatan ofishin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Farfesa Muhammad Ibn Abdallah; da Hajiya Yardada Maikano Bichi, mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin mata.
Yadda Wasu Yan Nijeriya Suka Yi Kashin Ƙulli 116 Na Hodar Ibilis A Gaban Jami’an NDLEA
Sanata Barau ya bayyana cewa shirin tallafin, wanda ke gudana karkashin Barau Ibrahim Jibrin Foundation (BIJF), ya kasance wani ginshiki wajen bunkasa ilimi ga matasa daga Kano da sauran sassan Najeriya. Ya ce a halin yanzu, sama da ɗalibai 70 na ci gaba da karatun digiri na biyu da na uku a kasashen waje karkashin shirin.
A jawabin da ya gabatar ta bakin Shugaban Ma’aikatansa, Sanata Barau ya gode wa shugabancin jami’ar karkashin mukaddashin Mataimakin Shugaban Jami’a, Farfesa Aminu Ado, bisa hadin kai da jajircewar da suka nuna wajen tabbatar da nasarar shirin.
Kungiyar dalibai ta NAKSS (Kungiyar Daliban Jihar Kano ta Kasa), reshen FUDMA, ta karrama Sanata Barau da lambar yabo ta musamman bisa gudummawarsa wajen raya ilimi da ci gaban matasa.
-
Labarai7 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai3 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai2 days ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
