Connect with us

News

‎Jami’in ‘Yan Sanda Da Wata Mata Sun Rasa Rayukansu Bayan Kwantena Ta Murkushe Adaidita Sahu 

Published

on

Container

Wata babbar mota mai ɗauke da kwantena mai tsawon kafa 40 ta murkushe wata adaidita Sahu a karkashin gadar Ijora Causeway, ranar Talata, inda wani jami’in ‘yan sanda da wata mata suka mutu nan take.

‎Rahotanni daga LASTMA sun nuna cewa hadarin ya faru ne yayin da direban motar mai rijista XP 368 AKD ke ƙoƙarin yin wani motsi mai haɗari, wanda ya yi sanadiyyar murkushe adaidita Sahu mai lamba KJA 364 QN.

Advertisement

An Kama Matar Da Ƙone Al’aurar Ƴar Shekara 5 Saboda Fitsarin Kwance A Bauchi

‎Mutanen da suka tsira, ciki har da direban adaidita t, sun samu raunuka a kafafu, an kuma kai su Asibitin Jimi Ogunyemi, Gasikiya, Ijora, ta hanyar LASAMBUS don samun kulawa ta gaggawa.

‎Wani abin lura shi ne tashin hankali da aka samu a wurin hadarin, inda wasu mutane suka yi ƙoƙarin kunna wuta a motar. Sai dai ‘yan sanda suka shiga tsakani don dawo da zaman lafiya da kare ma’aikatan agaji.

Advertisement

 

 

Advertisement

PLATINUM POST NEWS 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending