News
An Kama Wani Mutum Bisa Zargin Sayar Da Ɗansa Mai Kwanaki Biyar Da Haihuwa Kan ₦1.5m
Rundunar ‘yan sanda a jihar Ebonyi ta kama wani mutum mai suna Chukwuma Onwe bisa zargin sayar da jaririnsa mai kwanaki biyar da haihuwa kan naira miliyan ɗaya da rabi (₦1.5m).
Rahotanni sun ce Onwe, wanda mazaunin Nwezenyi-Igbeagu ne a karamar hukumar Izzi, ya sayar da jaririn ne ga wata mata mai suna C. Ugochukwu, wadda itama jami’an tsaro suka kama.
Jirgin Tawagar ‘Yan Wasan Super Eagles Ya Yi Saukar Gaggawa A Kasar Angola
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Joshua Ukandu, ya tabbatar da kama mutanen biyu a wata sanarwa da ya fitar a Abakaliki ranar Asabar.
“Mun kama wanda ake zargi kuma yana hannunmu. Ana ci gaba da bincike kan lamarin,” in ji SP Ukandu.
-
News6 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News4 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News6 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
