Connect with us

News

Shugaba Tinubu Zai Bar Abuja Zuwa Kasar Italiya 

Published

on

FB IMG 1726484065137

Shugaban ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu, zai bar Abuja ranar Lahadi, 12 ga Oktoba, zuwa birnin Rome na ƙasar Italiya domin halartar taron shugabannin ƙasashen Aqaba Process, wanda zai mayar da hankali kan matsalar tsaro a yankin Yammacin Afrika.

Sanarwar da mai magana da yawun shugaban, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce, taron, wanda zai fara a ranar Litinin, 14 ga Oktoba, zai haɗa shugabannin ƙasashe, jami’an leƙen asiri da na soji daga ƙasashen Afrika, da kuma wakilan kungiyoyin ƙetare da na ƙasa, domin tattaunawa kan ƙalubalen tsaro da ke ƙaruwa a yammacin nahiyar.

Advertisement

Jirgin Tawagar ‘Yan Wasan Super Eagles Ya Yi Saukar Gaggawa A Kasar Angola 

An kafa taron Aqaba Process tun a shekara ta 2015 ƙarƙashin jagorancin Sarki Abdullah II na Jordan, tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Italiya.

Manufarsa ita ce ƙarfafa haɗin kai kan yaƙi da ta’addanci da laifukan da ke da nasaba da shi a yankin Sahel da tekun Gulf of Guinea.

Advertisement

A yayin taron, shugabanni da masu ruwa da tsaki za su tattauna hanyoyin da za a bi don ƙarfafa tsaro a ƙasashen Afrika ta Yamma, da kuma yaƙi da ta’addanci na ƙasa da kuma ta teku. Haka kuma, za a tattauna yadda za a ƙalubalanci yada ra’ayoyin tsattsauran ra’ayi ta intanet da dakile hanyoyin da ake amfani da su wajen daukar matasa cikin kungiyoyin ta’addanci.

Shugaba Tinubu zai kuma yi tattaunawa ta musamman da wasu shugabanni domin samun mafita kan matsalar tsaro a yankin

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending