News
Ƙungiyar One Kano Agenda Ta Yi Fatali Da Shirye-shiryen Zanga-zangar Neman Sakin Nnamdi Kanu A Kano
Ƙungiyar One Kano Agenda ta yi tir da wani shirin yin zanga-zanga a Kano da wasu ƙungiyoyi ke shirya wa domin neman a saki jagoran haramtacciyar ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, wadda Daraktan Ƙulki na ƙungiyar, Abbas Abdullahi, da Sakataren ta, Barrister Mukhtar Musa, suka sanya wa hannu, ƙungiyar ta bayyana wannan shiri a matsayin abin zargi da kuma mai nufin tayar da hankalin jama’a.
KANFEST 2025: Gwamnatin Kano Ta Shirya Bikin Al’adu Da Fasaha Na Ƙasa Da Ƙasa
Ƙungiyar ta ce ko da yake yin zanga-zangar lumana na daga cikin ‘yancin da doka ta bai wa ɗan ƙasa, amma yin hakan a Kano — jihar da babu wata alaƙa kai tsaye da Nnamdi Kanu ko ƙungiyarsa — na iya zama wata makarkashiyar da aka kitsa domin tayar da hankali da kawo rudani.
“Shirin yin irin wannan zanga-zanga a Kano ba da niyyar neman adalci ake yi ba, sai dai don tada rikici da tayar da fitina a jihar,” in ji ƙungiyar a cikin sanarwar.
Ƙungiyar ta ce Nnamdi Kanu yana fuskantar shari’a a gaban kotu mai cikakken iko bisa laifuffuka da suka shafi cin amanar ƙasa, tayar da fitina, da aikata ayyukan ta’addanci, don haka neman a sake shi ta hanyar zanga-zangar titi na nufin raini da tauye aikin kotuna.
“Idan irin waɗannan abubuwa aka bari, zai zama kamar doka ta tsaya a gefe yayin da hayaniya ke rike madafun adalci,” sanarwar ta ƙara da cewa.
Ƙungiyar ta kuma yi tambaya kan dalilin da ya sa aka zaɓi Kano a matsayin wurin zanga-zangar, tana mai cewa hakan wata manufa ce da aka shirya domin jawo jihar cikin rikici da tashin hankali.
“Kano ba filin gwaji ba ne ga masu son kawo rudani. Mutanen Kano sun yi manyan ƙoƙari wajen kare zaman lafiya, kuma ba za mu bari a jawo su cikin tashin hankali ba,” in ji sanarwar.
Ƙungiyar ta bukaci hukumomin tsaro da su dauki matakai kafin lokaci domin hana kowane taron da zai iya kawo tashin hankali, tare da kiran Gwamnatin Jihar Kano da ta sa ido kan duk wani motsi da zai iya lalata zaman lafiya.
Haka kuma, ta roƙi matasan Kano da su guji duk wani yunkuri na amfani da su a matsayin kayan wasa wajen aikata abin da zai kawo rikici ko ɓata sunan jihar.
“Zaman lafiya a Kano abu ne mai daraja. Duk wanda ke ƙoƙarin kawo rikici dole ne a bayyana shi kuma a ɗauki mataki a kansa,” sanarwar ta jaddada.
A ƙarshe, Ƙungiyar One Kano Agenda ta tabbatar da jajircewarta wajen kare zaman lafiya, adalci da bin doka, tana mai cewa “ba wanda ya fi doka ƙarfi, kuma adalci dole ne a nemi ta hanyar kotu, ba ta hanyar titi ba.”
