News
KANFEST 2025: Gwamnatin Kano Ta Shirya Bikin Al’adu Da Fasaha Na Ƙasa Da Ƙasa
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da shirye-shiryen gudanar da babban bikin al’adu da fasaha na farko a tarihin jihar da ake kira KANFEST (Kalankuwa) 2025, wanda za a gudanar daga ranar 25 zuwa 27 ga Oktoba, 2025, a Kano Trade Fair Complex.
Bikin, wanda Ma’aikatar Al’adu da Yawon Buɗe Ido ta Jihar Kano ke shiryawa ƙarƙashin kulawar Mataimakin Gwamna, Kwamared Aminu Abdussalam, zai gudana ne da taken “Kare Tarihi, Don Gina Gaba.”
An Kammala Zagaye na Hudu (4) na Rigakafin Cutar Cizon Sauro (Malaria) a Fadin Jihar Kano
A cewar Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, wannan gagarumin taro zai kasance dandali na haɗa masu fasaha, ƙungiyoyin al’adu, masu saka jari, da baƙi daga sassan ƙasar nan da ƙetare domin raya al’adun Kano da haɓaka tattalin arziki ta hanyar yawon buɗe ido.
“KANFEST ba wai nishaɗi kaɗai ba ne, amma wata dama ce ta farfaɗo da al’adunmu, ƙarfafa haɗin kai, da haɓaka tattalin arzikin al’umma,” in ji Waiya
Ya ce bikin zai zama wata hanya ta haɗa tsofaffin dabi’u da sabbin ƙirƙira don gina makomar al’umma, tare da amfani da al’adu a matsayin hanyar zaman lafiya da ci gaba.
Abubuwan da za su haskaka a KANFEST sun haɗa da:
Kokuwa ta gargajiya ta Kano – nuna ƙarfin da tarihin Hausawa ke alfahari da shi.
Nunin Sana’ar Fata ta Majema – wanda ya tabbatar da sunan Kano a kasuwannin duniya.
Ƙirƙirar Kayayyakin Fata na Dukawa – haɗin fasahar gargajiya da na zamani
“Dukkan Kabilu, Dandalin Ɗaya” – alamar haɗin kai da mutunta bambancin al’umma.
Kwamishinan ya ce, “Gwamnatin Kano ta ɗauki matakin mayar da al’adu ginshiƙin cigaba. Daga bikin al’adu zuwa jari na ƙasa da ƙasa — muna buɗe ƙofofi ga masu zuba jari don su ga damar da ke Kano.”
Ya kuma yi kira ga ‘yan ƙasa da ƙasashen waje da su halarci bikin domin su shaida ɗaukakar Kano a matsayin cibiyar al’adar Hausawa da wuri mai cike da tarihi, mutunci, da ƙirƙira.
“Haka ne, duniya za ta zo Kano ta hanyar al’adu,” in ji Waiya
