News
An Kammala Zagaye na Hudu (4) na Rigakafin Cutar Cizon Sauro (Malaria) a Fadin Jihar Kano
Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta kammala zagaye na hudu (Cycle 4) na shirin Rigakafin Cutar Cizon Sauro (Seasonal Malaria ChemopreventionSMC) a dukkan kananan hukumomi 44 na Jihar.
Wannan zagaye ya gudana daga ranar Lahadi 19 zuwa Laraba 22 ga watan Oktoba, 2025, tare da hadin gwiwar Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko da sauran abokan hulɗa a fannin lafiya.
MTN zai rufe ofisoshi 101 a Kano, Borno da Adamawa saboda gyare-gyare
Shirin SMC yana daga cikin muhimman matakan da Gwamnatin Jihar Kano ke ɗauka domin rage yaduwar cutar Malaria, musamman a tsakanin kananan yara masu shekaru tsakanin 5 da yanwatanni 3 zuwa 11. Aikin ya haɗa da zagayen gida-gida domin rarraba magungunan kariya da kuma wayar da kan jama’a game da muhimmancin rigakafi da tsaftar muhalli.
Ma’aikatar Lafiya ta bayyana cewa, kammala wannan zagaye na hudu ya zo ne daidai da lokacin da damuna ta ƙare kuma aka fara shigowa yanayin sanyi lokacin da yawan sauro ke raguwa. Duk da haka, Ma’aikatar ta jaddada muhimmancin ci gaba da tsaftace muhalli domin kaucewa ci gaba da yaduwar cutar.
A bana (2025), an samu gagarumar nasara a aiwatar da shirin, inda rahotanni daga sassan lura da lafiyar jama’a suka nuna raguwar yawan masu kamuwa da cutar Malaria a fadin jihar. Wannan nasara na nuni da tasirin haɗin kai tsakanin Gwamnati, ma’aikatan lafiya da Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko wajen kare lafiyar kananan yara da iyalai baki ɗaya.
Nasarar aikin ta samu ne sakamakon jajircewar ma’aikatan lafiya daga matakai daban-daban waɗanda suka yi aiki tukuru wajen tabbatar da gudanar da shirin cikin nasara da inganci.
Ma’aikatar Lafiya ta kuma yi gargaɗi ga jama’a da su ci gaba da tsaftace muhalli, tare da guje wa barin ruwa a buɗe ko kwance, domin hakan na iya zama matsugunin sauro ko da a cikin yanayin sanyi. An kuma tunatar da jama’a muhimmancin amfani da magungunan kariya da kuma gidan sauro (treated nets) domin kare iyalai daga cizon sauro da cutar Malaria.
A ƙarshe, Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Kwamishinan Lafiya, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ta gode wa ma’aikatan lafiya, abokan hulɗa, da al’umma baki ɗaya bisa haɗin kai da goyon bayan da suka bayar. Ma’aikatar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da shirye-shiryen lafiya masu inganci domin kare rayukan jama’a da tabbatar da lafiyar kowa a fadin Jihar Kano.
