Connect with us

News

K-MAN Ta Taya Rear Admiral Idi Abbas Murna Bisa Karin Matsayin Da Ya Samu 

Published

on

images (1)

Kano Media Advocacy Network (K-MAN) ta bayyana farin cikin ta kan nasarorin da Rear Admiral Idi Abbas, ɗan asalin jihar Kano, ya samu a rundunar sojin ruwa ta Najeriya da kuma karin matsayin da aka ba shi.

A cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na ƙungiyar, Munnir Ibrahim Publisher, ya fitar a madadin babban daraktan K-MAN, Sulaiman Ahmad Indabawa, ƙungiyar ta bayyana Rear Admiral Abbas a matsayin babban ɗan ƙasa mai kishin ƙasa, gaskiya da jajircewa a aikinsa.

Advertisement

Za A Yi Wa Karin Manyan Sojoji 60 Ritaya Bayan Sauke Hafsoshin Tsaro

An haifi Rear Admiral Idi Abbas a ranar 20 ga Satumba, 1969, a jihar Kano. Ya shiga rundunar sojin ruwa a matsayin Mid-Shipman a ranar 18 ga Satumba, 1992, karkashin Regular Course ta 40. Bayan shekaru da dama na aiki tukuru da kwarewa, an ɗaga shi zuwa matsayin Rear Admiral a ranar 10 ga Satumba, 2020.

A cikin aikinsa, Rear Admiral Abbas ya rike mukamai da dama masu muhimmanci, ciki har da Flag Officer Commanding, Central Naval Command, Yenagoa, jihar Bayelsa, inda ya jagoranci yaki da satar mai, fashin teku da sauran laifuka a yankin. Wannan aiki nasa ya taimaka wajen kare dukiyar ƙasa da tabbatar da tsaro da tattalin arziki.

Advertisement

Kungiyar K-MAN ta yaba masa a matsayin mutum mai tsantsar gaskiya, ƙwarewa da jajircewa, wanda ya zama abin koyi ga matasan Najeriya musamman na jihar Kano.

Kungiyar ta kuma yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta karrama Rear Admiral Idi Abbas ta hanyar shirya taron girmamawa (State Honours Dinner) domin nuna godiya bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen girmama jihar da ƙasa baki ɗaya.

Advertisement

“Muna taya Rear Admiral Idi Abbas murna da wannan nasara, kuma muna fatan Allah Ya ƙara masa nasara da ɗaukaka a sabbin nauyin da ke gabansa,” in ji sanarwar K-MAN.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending