Connect with us

News

Ƙungiyar Likitoci Ta Umarci Mambobinta Da Su Tsunduma Yajin Aiki A Faɗin Najeriya

Published

on

doctors (1)

Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta umarci mambobinta da su tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a ranar 1 ga watan Nuwamba.

Sabon shugaban ƙungiyar Mohammed Sulaiman, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a wannan Lahadi, inda ya umarci mambobin ƙungiyar a duk faɗin Najeriya da su shirya domin fara yajin aikin daga ranar 1 ga watan Nuwamba mai zuwa.

Advertisement

Yan Sanda Sun Kama Mutane 2 Da Ake Zargi Da Alaka Da ‘Yan Bindiga A Kano

A cewar Mohammed, sun ɗauki wannan mataki ne bayan ƙarewar wa’adin kwanaki 30 da suka bai wa gwamnatin ƙasar, ba tare da ta waiwaye su ba.

Wannan mataki dai, na zuwa ne bayan cimma matsaya a taron ƙolin ƙungiyar da shugabanninta suka shafe sa’a biyar suna tattaunawa a ranar Asabar.

Advertisement

A baya dai, ƙungiyar ta bai wa gwamnatin ƙasar wa’adin kwanaki 30 don biya mata jerin buƙatun ta, da ta ɗauki alƙawari a baya, tare kuma da fito da wasu tsare-tsaren da za su bunƙasa walwalar mambobinta.

Dama dai, gabanin kwanaki 30 ɗin da ƙungiyar ta bayar, a lokuta mabambanta ta ba wa Gwamnatin Tarayyar Najeriya, wa’adi kafin ta shiga yajin aikin gargaɗi a ranar 12 ga watan Satumban da ya gabata.

Advertisement

Da farko ƙungiyar ta ba da wa’adin kwanaki 21 a watan Yulin 2025, sannan ta sake ba da wani wa’adin na kwanaki 10 wanda ya ƙare a ranar 10 watan Satumba, sai kuma wa’adin sa’o’i 24 da ta sake ba wa Gwamnatin gabanin shiga yajin aikin da suka kawo ƙarshensa a ranar Lahadi 14 ga watan Satumbar 2025.

Haka zalika bayan janyewar a ranar 14 ga Satumban da ya gabata, sun sake ba wa gwamanatin ƙasar wa’adin mako biyu, da ta cika alƙawarin da ta ɗauka na biya musu sauran buƙatunsu, in ba haka ba za su zunduma wani yajin aikin, wanda gabanin ƙarewarsa sabon shugaban ƙungiyar Mohammed Sulaiman, ya sanar da sabon wa’adi har kwanaki 30 daga ranar 1 ga wannan wata Oktoba.

Advertisement

 

 

Advertisement

FRI HAUSA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending