News
Yan Sanda Sun Kama Mutane 2 Da Ake Zargi Da Alaka Da ‘Yan Bindiga A Kano
Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kano ta bayyana kama wasu mutane biyu da ake zargin suna da alaka da ‘yan wata kungiyar barayin daji da ke addabar wasu yankuna.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana a wata sanarwa cewa an gudanar da samamen ne da hadin gwiwar rundunar yaki da satar mutane domin neman kudin fansa, tare da hadin gwiwar ofishin ‘yan sanda na Shanono.
Wata Tirela Ɗauke Da Kayan Buga Takardu Ta Faɗo Daga Saman Gada
SP Kiyawa ya kara da cewa an samu bayanan sirri daga al’ummar Farin Ruwa da suka nuna cewa an ga wasu take-take da ba a gamsu da su ba, wadanda ake zargin na iya zama shigowar ‘yan bindiga a yankin.
Sanarwar ta ce Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa al’ummar yankin saboda wayar da kai da kuma bayar da bayanai, sannan ya tabbatar da cewa rundunar na ci gaba da gudanar da bincike domin kamo sauran ‘yan bindigar da ke ɓoyewa a jihar.
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News17 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
